Ran 27 ga wata, bangarori 3 da ke yin daidaituwar hargitsin Darfur wato kungiyar tarayyar Afrika da kawancen Turai da kasar Chadi sun kirayi bangarorin da ke gwabzawa na shiyyar Darfur da su daina duk aikace-aikacen yin nukura da juna, su yi biyayya sosai ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka daddale a watan Afrilu na bana.
A birnin N'Djamena, babban birnin kasar Chadi, bayan an kiran taron kwamitin hadin kai na sa ido kan tsagaita bude wuta cikin shiyyar Darfur, bangarorin 3 sun bayar da wata sanarwa, inda suka nuna cewa, ya kamata bamgarorin da ke gwabzawa na Darfur su daina bude sabon filin yaki waje da shiyyar da aka kayadde, kuma su ba da taimako ga 'yan gudun hijira masu yawan miliyoyi da kare su.(ASB)
|