|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2004-11-24 21:27:42
|
 |
Shugaban Kawancen Kasashen Afirka yana ganin cewa, tsarin duddubawar juna ya ba da taimako wajen bunkasa kasashen Afirka
cri
Ran 23 ga wata, shugaban Kawancen Kasashen Afirka kuma shugaban kasar Nijeriya Mr. Olusegun Obasanjo da ke halartar taron shugabanni na shirin sabon kawance domin bunkasa nahiyar Afirka a birnin Algiers, babban birnin kasar Algeria ya bayyana cewa, cim ma nasarar aiwatar da tsarin duddubawar juna a tsakanin kasashen Afirka ya kara amincewa a fannonin raya tattalin arzikin kasashen Afirka da neman samun kwanciyar hankali da aikin tafiyar da dimokuradiyya.
Mr. Obasanjo yana ganin cewa, tsarin duddubawar juna a tsakanin kasashen Afirka ya taka muhimmiyar rawa a fannonin sa kaimi ga kasashen Afirka da su tafiyar da manufofi masu kyau da kyautata halin tattalin arzikin zaman al'umma da kuma fitar da nahiyar Afirka daga bakin tabarbarewa. Ya kuma ba da sanarwa cewa, za a yi taron shugabanni na tsarin duddubawar juna a tsakanin kasashen Afirka a kasar Masar a watan Afril na shekara mai zuwa.(Tasallah)
|
|
|