A ran 23 ga wata a birnin Aljiers, wato babban birnin kasar Aljeriya an fara taron shugabannin kasashen Afirka na game da "Sabon shirin abokantaka na raya Afirka".
A gun taron, za a duba yadda ake tafiyar da tsarin dudduba juna a tsakanin kasashen Afirka, da kuma za a gabatar da ra'ayoyin kyautata wannan tsari. A watan Maris na shekarar 2003 ne aka kafa tsarin nan.
Makasudin tafiyar da "Sabon shirin abokantaka na raya Afirka" shi ne kau da talauci daga Afirka da cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa a Afirka. Shugabanni 14 na kasashen Afirka ciki har da shugaba Abdelaziz Bouteflika na kasar Aljeriya suna halartar wannan taro. (Sanusi Chen)
|