Ran 22 ga wata Mr.Mustafa Othman Ismail ministan harkokin waje na kasar Sudan ya zargi 'yan dakaru yin adawa da gwamnati na Darfur da sun ki yarjejeniyar tsagaita bude wuta, saboda suna cigaba da kai farmaki ga zango na 'yan gudun hijira.
Ya ce, wasu 'yan dakaru yin adawa da gwamnati sun kai farmaki wani zango na 'yan gudun hijira da ke gabashin Darfur, nufin neman motar 'yan sanda da ke ciki. 'yan sanda sun bude wuta kuma sun kashe 'yan dakaru guda hudu, 'yan sanda guda hudu su mutu. Wasu 'yan dakaru daban su kai farmaki ga wani wurin daban, kuma kashe wasu 'yan sanda.
Mr.Ismail ya ce, gwamnatin Sudan ya riga ya gayawa jami'in kungiyar tarayyar kasashen Afirka mai lura da sassan biyu da su tsagaita bude wuta.
|