Ran 22 ga wata, sojojin kula da zaman lafiya da MDD ta aika zuwa Kongo don ba da taimako sun sauka birnin Kinshasa, za a shimfida sojojin a gabashin Kongo Kinshasa.
An ce, MDD za ta aika da sojojin kula da zaman lafiya fiye da 5000 zuwa Kongo Kinshasa, galibinsu sun zo daga kasar India da kasar Pakistan.
Watan Okatoba na bana, kwamitin sulhu na MDD ya zartar da kudurin kara karfin sojojin ba da taimako da ke Kongo Kinshasa. Aikin sojojin sun kunshe da "hana rikicin tashin hankali a inda halin maras lafiya" da "ba da taimako ga mutanen dake cikin hadarin rikicin" da "kwashe makaman da aka mika wa gabashin kasar ba na halak ba". Kudurin kuma ya ba da izni ga sojojin da su iya dauki duk matakan da ana bukatar don aiwatar da aikin.[Musa]
|