Ran 19 ga wata, an rufe taron musamman na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan batun kasar Sudan wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya. A gun taron, an zartas da kuduri don neman bangarori biyu masu gwabzawa da juna na kudancin kasar Sudan da su daddale yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe a tsakaninsu tun da wurwuri.
A wannan rana, a birnin Nairobi, gwamnatin kasar Sudan da kungiyar kwatar 'yancin jama'ar Sudan wadda ke yin adawa da gwamnati a kudancin kasar sun sa hannu a kan takardar tabbatar da tsagaita bude wuta, kuma sun dauki alkawari cewa, bangarorin nan biyu za su kulla yarjejeniyar daina yakin basasa da aka shafe shekaru 21 ana yinsa a kasar Sudan kafin ran 31 ga watan gobe. Mr Amr Mussa, babban sakataren Kawancen Kasashen Larabawa ya bayar da sanarwa a birnin Alkahira don yin maraba da wannan. (Halilu)
|