Malariya wata tsohuwar cuta ce. A cikin shekaru 100 da suka gabata, likitoci na duk duniya suna ta neman hanyar da za a bi a kau da ita. Bisa labari da dumi dumi da WHO, wato kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayar, ana samun masu cutar nan miliyan 600 wadanda suke tsananin bukatar jiyya, kuma ko wace shekara, yawan mutanen da suka mutu a sakamakonta ya zarce miliyan 3. A ciki, mutanen Afirka da suka kamu da cutar sun kai 90% na wannan adadin. Sabo da haka, ana ganin malariya kamar muguwar cuta ce ta farko a Afirka, kuma muhimmin abu ne da yake ta kawo wa rayukan mutanen Afirka barazana, kuma tana dakatar da bunkasuwar tattakin arzikin kasashen Afirka. A ran 25 ga watan Afril na shekarar 2000, a Abuja, wato babban birnin kasar Nijeriya, shugabanni da manyan jami'ai na kasashen Afirka 53 sun yanke shawarar mai da ran 25 ga watan Afril na ko wace shekara ya zama ranar yaki da cutar malariya ta Afirka.
A shekarar 1973, bisa nazarin da aka yi, an kirkiro wani sabon maganin cutar malariya da ake kira Artemisinin a kasar Sin. Kuma gwajin da aka yi ya nuna cewa, Artemisinin yana iya warkar da 95% na masu ciwon malariya, kuma har zuwa yanzu, kwayoyin cutar malariya ba su da karfin kin maganin nan. Kasar Sin ta sami mayan nasarori wajen maganin cutar malariya. Bisa kokarin da ta yi cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta sami nasarar rage yawan mutanen da suka kamu da cutar malariya a ko wace shekara daga miliyan 30 kafin samun 'yancin kan kasar zuwa dubu 100 a halin yanzu. A shekarar 2001, kungiyar kiwon lafiya ta duniya, ta amince da cewa, Artemisinin da kasar Sin ta kirkiro yana da amfani sosai wajen yaki da cutar malariya. Har ma asusun maganin cututtukan Sida da tibi da malariya na duniya ya umurci kasashe 34 da su yi amfani da Artemisinin a maimakon kuni da sauran magungunan gargajiya, kuma ya shirya zai sayi Artemisinin da darajarsa ta kai dollar Amurka miliyan 450 a cikin shekaru 5 masu zuwa. Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta kimanta cewa, ya zuwa shekarar 2005, za a bukaci alluran Artemisinin da yawansu ya kai miliyan 100, amma a halin yanzu, an samu 1/3 na wannan adadi kawai. Wannan kuma ya samar da filin da za a yi hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka don yaki da malariya.
Don tabbatar da "shirin Addis Ababa" da aka zartar da shi a gun dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kasar Sin tana so ta bayar da taimakonta wajen yaki da cutar malariya, ta gabatar da Artemisinin da fasahohinta na yaki da malariya zuwa shiyyoyi daban daban na Afirka bisa shirye shirye kuma mataki bisa mataki, ta yadda za a kau da wahalar malariya da mutanen Afirka suke sha da barazanar da malariya ke kawo wa rayukansu. Ban da wannan kuma, a cikin shekaru gamai da suka wuce, kasar Sin ta ba da babban taimakon jiyya ga kasashen Afirka, kuma a halin yanzu, kungiyoyin ba da taimakon jiyya na kasar Sin suna aiki a kasashe 34 na Afirka, sabo da haka, sun sami hakikanan rahotanni da yawa game da halin cutar malariya da ake ciki a kasashen Afirka inda suke girke. Kuma za a iya yin amfani da wadannan kungiyoyi don a yi bincike a kan halin kamuwa da cutar malariya a kasashen Afirka, ta yadda za a samar da wani dandalin yin musanyar labarai da fasahohi da kuma kwararru, kuma a horar da jami'an musamman na maganin malariya da likitoci ga kasashen nan, kuma a tsara manufofin maganin cutar nan gare su.
A takaice dai, idan an tabbatar da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin yaki da malariya bisa tsare-tsaren dandalin tattaunawa na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, da gabatar da Artemisinin da fasahohin kasar Sin na yaki da cutar nan zuwa kasashen Afirka, to, za a kawo wa mutanen Afirka alheri, haka kuma zai nuna sahihancin kasar Sin wajen tafiyar da ayyukan da za a yi bayan da aka kammala dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Afirka .(Lubabatu)
|