Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-10-27 21:34:51    
Kasar Sudan ta yarda da kawancen kasashen Afirka ta kara aika da sojoji da 'yan kallo a shiyyar Darfur

cri
A ran 26 ga wata, majalisar dokokin kasar Sudan ta yarda da kawancen kasashen Afirka ya kara aika da 'yan kallo da sojoji a shiyyar Darfur domin sa ido kan yadda bangarori masu adawa da juna za su aiwatar da yarjejeniyar kawo kashen wutar yakin a shiyyar.

A gun taron majaliasar dokokin kasar, minista mai kula da dangantakar yin cudanya da kasashen waje Mr. Mustafa Othman Ismail ya yi jawabi, inda ya ce, kawancen kasashen Afirka zai kara aika da 'yan kallo 450 da sojoji fiye da 2300 da 'yan sanda fiye da dari 5 da sauran farar hula zuwa shiyyar Darfur. Wadannan za su zo daga kasashen Najeriya da Rwanda da Afirka ta Kudu da Burkinafaso. Nauyinsu shi ne za su sa ido kan yadda bangarori daban-daban masu adawa da juna za su aiwatar da yarjejeniyar kawo karshen wutar yaki domin kafa sharadi don aikin sa ayar wutar yaki a shiyyar da fara yin aikin sake gina shiyyar. (Sanusi Chen)