A ran 26 ga wata, mataimakin kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amirka Mr. Adam Ereli ya ce, yanzu ana gaggauta ana yin aikin aika da sojojin kawancen kasashen Afirka zuwa shiyyar Darfur ta kasar Sudan.
Mr. Ereli ya fadi haka a gun wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana. Mr. Ereli ya ce, yanzu ana tsara shirin karshe kan yadda sojojin kawancen kasashen Afirka za su iya dauki jiragen sama zuwa Sudan. A cikin gajeren lokaci mai zuwa ne za a iya tafiyar da wannan shiri. Mr. Ereli ya kara da cewa, wannan ya bayyana cewa, a karkashin taimakon al'ummar duniya, kawancen kasashen Afirka tana ba da muhimmiyar gudummawa wajen ba da taimako da tabbatar da zaman karko a yankin da yake.
Bisa shawarar da Mr. Kofin Annan, wato babban sakataren MDD ya bayar, a ran 15 ga watan da muke ciki, kawancen kasashen Afirka ya shelanta cewa, zai kara aika da sojoji 4500 zuwa shiyyar Darfur ta kasar Sudan. Ya kuma yi fatan za a iya gama aikin matsuguni wadannan sojoji a karshen watan Nuwamba mai zuwa. (Sanusi Chen)
|