Ran 25 ga wata, shugaban kasar Afirka ta kudu Mr.Thabo Mbeki ya gana da shugaban babban jam'iyyar hamayyar kasar Zimbabwe Mr.Morgan Tsvangirai don tattaunawa kan dabarar warware matsalar siyasa ta kasar.
Kakakin shugaban kasar Afirka ta kudu Mr.Bheki Khumalo ya ce, wannan tattaunawa shi ne wani kashi na tattanunawar da ke tsakanin shugba Mbeki da duk sassa siyasa na kasar Zimbabwe, amma kakakin bai ce kome ba kan abin dake cikin tattaunawar.
|