Ran 25 ga wata a birnin Abuja hedkwatar kasar Nijeriya an fara yin shawarwari na karo na biyu don tattaunawar yaya za a iya warware matsalar Darfur wanda Kungiyar Kasashen Afirka ta shirya tsakanin gwamnatin da kungiyoyi 2 na yan dakarun yin adawa da gwamnati.
Kafin taron tattaunawar, kakakin kungiyar wakilan gwamnatin Sudan Mr.Ibrahim ya ce, gwamnatin zai warware matsalar Darfur da iyakancin kokarinsa, kuma yana da kyakyawan fatan samun cigaban tattaunawar. Kakakin yan dakarun yin adawa da gwamnati mai suna "Justice and Equality Movement" da Mr.Ahmed Mohammed Tugod sun bayya cewa suna fatan sabon tattaunawar za ta sami cigaba.[Musa]
|