Ran 24 ga wata a babban birni Khartoum na Sudan Mr.Solana babban wakilan kula da harkokin manufofin harkokin waje da na tsaro na Kungiyar gamayar Turai ya ce, kungiyar gamayar Turai ta yi maraba da kokarin da kungiyar kasashen Afirka ta yi don warware matsalar Darfur.
Mr.Solana ya yi jawabin na a taron manema labaru kafin ya gama aikin ziyararsa a Sudan. Kuma ya yi kira ga kwamnantin Sudan da yan dakarun yin adawa da gwamnati don su daddale yarjejeniyar zaman lafiya, kuma yana fata tattaunawar zaman lafiya da ke tsakaninsu da tattanawar da ke tsakanin gwamnatin Sudan da jam'iyyar hamayya ya sami cigaba.[Musa]
|