Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2003-09-30 23:00:27    
Sashen Hausa

cri

    Ran 1 ga  watan Yuni na shekarar 1963, aka fara watsa labarai da harshen Hausa ga mutanen Afrika.  Yanzu muna watsa shirye-shiryenmu sau 2 kowace rana, kuma kowane shiri mu kan yi shi cikin rabin sa'a.   Kowane shiri ya kasu kashi biyu.  Kashi na farko mu kan watsa labarai na gida da na duniya da kuma sharhohi.  Kashi na karshe kuwa, mu kan gabatar muku da shirye-shiryen musamman ko bayanai don ilmantarwa.

    Yanzu Sashen Hausa yana da ma'aikata Sinawa 13 wato maza 8 da mata 5.  Sunayen ma'aikatansu su ne Halima (Wang Dangchun), da Asabe (Zhao Xiaoqun), da Hadiza (Yuan Xinfeng), da Jamila (Zhou Huang), da Bilkisu (Xin Yuhui), da Usman (Sun Deyi), da Umaru (Qiu Dianqing), da Halilu (Dong Hongyuan), da Ali (Tian Zongzong), da Sani (Wang Zhihong), da Dogong Yaro (Sun Hejun), da Sanusi (Chen Liming), da Ado (Li Shouming).   Bahaushen da ke aiki yanzu a sashenmu shi ne Balarabe Shehu Ilelah, kuma shi mutumin birnin Bauci ne a Nijeriya. Bahaushe nan 'dan Nijeriya yana ba mu taimako mai yawa ta fannin gyara bayananmu, da fassara labarai da kuma gabatar da shiriye-shiriye.  Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin yana yi masa godiya sosai, tare da sauran Hausawan da suka zo suka taimaka mana.

    Wata guda kawai bayan mun fara watsa shirinmu na Hausa, sai muka samu wasika ta farko daga Nijeriya. Yanzu kowace rana mu kan samu wasiku masu tarin yawa daga wajen masu sauraronmu. Kuma wasikunku sai karuwa suke yi shekara da shekaru.  Don haka, Sashen Hausa na Rediyon Kasar Sin yana godiya ga duk wadanda ke sauraronmu ko kuma aiko mana wasiku tare da gabatar mana da shawarwari. Muna fata za ku ci gaba da karfafa zumuncin dake tsakanin jama'ar kasar Sin da ta kasashen Afrika.